Kasuwanci

Informações:

Sinopsis

Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.

Episodios

  • Koken 'yan Najeriya na rashin saukar farashin kayan masarufi duk da faduwar Dala

    24/04/2024 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan batun korafin ‘yan Najeriya ke yi game da rashin ganin sauyi a farashin kayan amfanin yau da kullum, bayan karyewar farashin ƙudaden ƙetare masamman dalar Amurka da sanadin tashin ta ne ya haddasa mummunan tashin farashin kayayyaki a kasar, wanda har hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce lamaarin ya yi muni. Ko da ya ke a wasu manyan biranen Najeriya irinsu Legas da Abuja, an fara ganin sauƙi a wasu kayayyakin abinci irinsu shinkafa da man girki da dai sauransu.Ku latsala alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba........

  • Yadda matasa suka rungumi kananan sana’o’i lokacin azumin Ramadana a Damagaram

    03/04/2024 Duración: 09min

    Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan kananan sana’o’i da matasa ke yi don samun na abinci a lokacin azumin watan Ramadana a Damagaram da ke jamhuriyar Nijar. wasu daga cikin sana'oin da matasan sukafi mai da hankali akai dai sun hada da bredi ko kayan marmari ko kayan lambu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......

  • Gidauniyar Dangote ta kashe naira biliyan 15 na tallafin abinci a Najeriya

    27/03/2024 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan rabon tallafin abincin naira biliyan 15, da Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar a Najeriya. Wannan dai na daga cikin matakan rage radadin talauci a tsakanin al'ummar Najeriya, da gidauniyyar hamshakin attajirin Afirka ta kaddamar a birnin Kano da ke arewacin kasar. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......

  • Yadda matsin rayuwa ya tilastawa 'yan Najeriya fasa rumbunan abinci

    06/03/2024 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yada zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya yi dubi kan matsanancin kuncin rayuwar da al’umman kasar suka shiga da har ta kai ana fasa rumbunan abinci ko tare manyan motocin dakon kaya a tituna ana kwasan abinci.

  • Yadda al'ummar kasashen yammacin Afrika ke kokawa saboda tsadar rayuwa

    28/02/2024 Duración: 09min

    A wannan makon shirin Kasuwa akai miki dole, zai yi duba ne game da bakar ukubar da al’ummar kasashen Nahiyar Africa ke fuskanta, a sanadiyar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, musamman kasashen Nijeriya, Nijar da kuma Cameroon. Yanzu haka dai a iya cewa wannan yanayi na hauhawar farashin kayan masarufi tuni ya zame wa kasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da kuma Cameroon Dan zani a kasuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa.....

  • Yadda Najeriya ke neman taimakon Bankin Duniya don farfado da tattalin arziki

    13/02/2024 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa a kai miki dole tare da Rukayya Abba Kabara a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Najeriya ke neman taimakon bankin duniya a wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin kasar da ke fuskantar tarnaki. Tattalin arzikin na Najeriya na ci gaba da durkushewa ne duk da kasancewarta mafi karfin tattalin arziki kuma mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika, dalilan da ake alakantawa da yankewar yawan man da kasar ke fitarwa baya ga ci gaba da zangewar darajar kudin kasar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

  • Faduwar darajar Naira ta tsayar da harkokin 'yan canji a makwaftan Najeriya

    07/02/2024 Duración: 10min

    Shirin 'Kasuwa a kai miki dole' na wannan mako ya tattauna akan yadda faduwar darajar Naira ke haddasa koma bayan kasuwar 'yan canji a makwaftan Najeriya.

  • Dalilan soke lasisin wasu kamfanonin wutar lantarki

    31/01/2024 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa a Kai Maki Dole na wannan mako, ya mayar da hankali ne a game da batun wutar lantarki a Najeriya, bangaren da ke fama da matsalololi tsawon shekaru.Shirin zai yi dubi ne a game da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na sokewa da kuma sabunta lasisi ga wasu kamfanonin da ke da alhaki rarraba wuta a cikin kasar.

  • Yadda faduwar darajar Naira ke yin illa ga kasuwanci a Najeriya

    24/01/2024 Duración: 09min

    Shirin 'Kasuwa a kai miki dole' na wanna makon ya mayar da hankali akan faduwar darajar naira da ke ci gaba da yin illa ga harkokin kasuwanci a sassan Najeriya. Wakilinmu a jihar Kano Abubakar Abdulkadir Dangambo ya duba yadda matsalar ke yin tasiri musamman babbar kasuwar hatsi ta Dawanau da ke Kano, wadda ke tattara 'yan kasuwa daga Najeriya da kuma kasashe irin su Chadi da Kamaru da Nijar da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

  • Yadda rufe iyakar Benin ya haifar da tsadar rayuwa a Nijar

    22/11/2023 Duración: 09min

    Shirin "Kasuwa akai Miki dole" na wanan mako tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Dosso dake Jamhuriya Nijar, yankin da ke kan iyaka da birnin Cotonou na Jamhuriya Benin inda jama'a suka shiga matsanancin halin tsadar rayuwa tare da kariyar tattalin arziki, sakamakon takun-kuman da Kungiyayoyi irinsu ECOWAS ko CEDEAO suka laftawa kasar, saboda Juyin mulkin da Sojoji sukayi. A Ranar 9 ga Watan Octoba da ya wuce Jamhuriya Benin ta rufe iyakar dake tsakaninta da makwabciyarta Jamhuriyar Nijar, bayan matakin da Kungiya ECOWAS ko CEDEAO ta dauka bayan da sojoji suka karbe mulki Ranar 26 ga watan Yuli wajen hambarar da shugaban Mohamed Bazoum.Jamhuriyar Bénin ta dauki matakin soke duk wata hulda cinikaya da gwamnatin sojin Nijar.Wanan matakin dai ya janyo hauhawa farashin Kayan bukatun jama'a na yau da kullun tare da haifar da koma bayan tattalin arziki a wasu sassan kasar, masamman  yankin Dosso, jiha daya tilo a Nijar da ta yi iyaka da Bénin har tsawan kilimita 150 daga yammacin Kasar.

  • 'Yan Najeriya na cikin matsin tattalin arziki tun bayan janye tallafin mai

    15/11/2023 Duración: 09min

    Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan hauhawar farashin kayyaki da ake fama da shi a Najeriya, wanda ya jefa al'umma masu karamin karfi cikin halin kunci. A Najeriyar tun bayan janye tallafin man fetir da kuma matsalolin rashin kudaden waje masamman dalar Amurka sun tsunduma kasar cikin mummunar hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni, lamarin da ya jefa al’ummar kasar musamman masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.Alkaluman hukumar kididdigar Najeriya na watan Satumba sun nuna cewa hauhawan farashin kayayyaki ya kai kashi 26.72, wanda masana ke gargadin zai iya kaiwa da kaso 30 cikin 100 nan da watan Disamba muddun ba’a kai ga gano bakin zarenba.Domin duba girman matsalar hauhawan farashin, RFI Hausa ya leka kasuwar Mile 12 International dake birnin Legas, daya daga cikin manyan kasuwannin kayan abinci da gwari a kasar.

  • Yadda masu kiwon kaji a Najeriya ke rufe gonakinsu saboda tsadar kayan abinci

    01/11/2023 Duración: 09min

    Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar abincin kaji ke tilastawa masu kiwon su rufe gonaki a tarayyar Najeriya, sakamakon asarar da suke tafkawa.

  • Yadda aka sake bude kasuwar Monday Market a jihar Borno

    25/10/2023 Duración: 10min

    Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan sake bude kasuwar Monday Market mai matukar muhimmanci a jihar Borno ta tarayyar Najeriya. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba

  • CISLAC ta horas da 'yan majalisun Najeriya kan muhimmacin haraji ga kasa

    18/10/2023 Duración: 09min

    Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan jan hankali da kungiyoyi irinsu CISLAC ke yi a Najeriya, wajen ganin gwamnati ta maida hankali kan gibi da ake samu a fannin tara haraji domin samun kudaden shiga. Masana sun yi ittifakin cewar Najeriya na da dimbin arzikin da bai kamata ace sai ta ciyo bashin kudade kafin biyan bukatun ta ba, amma sakaci da kuma cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu ke mayar da ita baya.Wannan yasa kungiyar CISLAC mai zaman kanta da ke sa ido kan ayyukan majalisar dokoki da kuma yaki da rashawa, da hadin guiwan cibiyar horar da ‘yan majalisun dokoki da demokuradiyya, suka shirya taro don horarwa da nunawa ‘yan majalisu rawar da za su taka wajen yin dokoki da saka ido a hanyoyin samar da haraji ga kasa.

  • Yadda Proparco ta ba da gudummuwa ga tattalin arzikin Najeriya cikin shekaru 15

    17/10/2023 Duración: 09min

    Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon ya mayar da hankali ne kan bukin cika shekaru 15 cibiyar bada lamuni da raya kasashe ta kasar Faransa Proparco ta yi ta na gudanar da ayyukanta a Najeriya, inda ta zuba jarin da ya kai dala biliyan daya a kasar cikin shekarun. Shirin zai mayar da hankali ne kan yadda ayyukan cibiyar ke bayar da gudunmawa ga fannonin daban-daban na ci gaban tattalin arzikin Najeriya. Tun bayan kafa cibiyar a shekarar 2008 a Najeriya, Proparco ta mai da hankali wajen hadin gwiwa da cibiyoyin hada-hadar kudi na cikin gida da na wasu kasashen Afirka wajen zuba hannun jari ga kamfanoni masu tasowa da sabbin kafuwa a fannin makamashi mara gurba da muhalli da harkokin noma da kere-kere da kiwon lafiya da dai sauransu…

  • Jiragen ƙasa sun fara jigilar kayayyaki daga Legas zuwa Ibadan

    20/09/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Kasuw akai Miki Dole na wannan makon ya tattauna ne kan yunkurin gwamnatin Najeriya na rage cunkuso a tashar jiragen ruwan ta Apapa da ke birnin Legas, wajen kaddamar da aikin soma kwashe kwantenoni daga tashar zuwa Ibadan da jirgin kasa na zamani.

  • Yadda kwanaki 100 na gwamnatin Tinubu ya riski ƴan Najeriya

    13/09/2023 Duración: 10min

    Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan mastin halin rayuwa da 'yan Najeriya suka shiga kwanaki 100 bayan kafa gwamnati. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba

  • Matsunta a Kamaru sun bukaci dage haramcin kamun kifi a Lagdo

    06/09/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako, ya leka ne jamhuriyar Kamaru, inda matsunta da ‘yan kasuwa suka bukaci dage dabi’ar gwamnati kan dokar haramta kamun kifi na tsawon watanni uku - uku da ake yi a duk shekara, wanda ya kai ga gudanar da zanga-zanga a garin Lagdo dake arewacin kasar.

  • Tasirin tattalin arzikin shigar sabbin kasashe kungiyar BRICS

    02/09/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako ya maida hankali ne kan taron Kungiyar BRICS ta kasashe masu tasowa wadanda suka kunshi Brazil da Rasha da India da China da kuma Afirka ta Kudu, wanda aka kafa ta domin kalubalantar kaifin tattalin arzikin kasashen yammacin duniya, wadda ta amince da shigar da sabbin kasashe shida cikinta amatsayin mambobi, wato Saudiyya da Iran da Habasha da Masar da Argentina sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa. 

  • Janye tallafin mai: Ta yaya tallafin gwamnatin Najeriya zai kai ga marasa galihu?

    23/08/2023 Duración: 10min

    Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako ya yada zango ne tarayyar Najeriya, inda Gwamnatin kasar ta ware kusan Naira biliyan 200, wanda ta rabawa jihohi 36 na kasar da birnnin tarayya Abuja da kuma motocin shinkafa, domin ragewa talakawa radadin da janye tallafin man fetur ya jefasu ciki. Ta yaya wannan tallafi zai kai ga marasa galihu, wadanda akayi dominsu? Abin da Shirin zai maida hankali akai kenan 

página 1 de 2