Kasuwanci

Informações:

Sinopsis

Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.

Episodios

  • Tasirin tattalin arzikin shigar sabbin kasashe kungiyar BRICS

    02/09/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako ya maida hankali ne kan taron Kungiyar BRICS ta kasashe masu tasowa wadanda suka kunshi Brazil da Rasha da India da China da kuma Afirka ta Kudu, wanda aka kafa ta domin kalubalantar kaifin tattalin arzikin kasashen yammacin duniya, wadda ta amince da shigar da sabbin kasashe shida cikinta amatsayin mambobi, wato Saudiyya da Iran da Habasha da Masar da Argentina sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa. 

  • Janye tallafin mai: Ta yaya tallafin gwamnatin Najeriya zai kai ga marasa galihu?

    23/08/2023 Duración: 10min

    Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako ya yada zango ne tarayyar Najeriya, inda Gwamnatin kasar ta ware kusan Naira biliyan 200, wanda ta rabawa jihohi 36 na kasar da birnnin tarayya Abuja da kuma motocin shinkafa, domin ragewa talakawa radadin da janye tallafin man fetur ya jefasu ciki. Ta yaya wannan tallafi zai kai ga marasa galihu, wadanda akayi dominsu? Abin da Shirin zai maida hankali akai kenan 

  • Farashin kayan abinci ya yi tashin goron zabi a duniya

    16/08/2023 Duración: 10min

    Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole na wannan makon ya yi nazari ne kan yadda ake ci gaba da samun hau-hawan farashin kayayyakin abinci a kasashen duniya musamman nahiyar Afrika. Masana sun bayyana cewa, yakin da ake fama da shi Ukraine na daya daga cikin manyan dalilan da suka haddasa tsadar farashin abinci a kasashen duniya, yayin da matsalar ke ci gaba da kamari a nahiyar Afrika saboda karin dalilai da suka hada da hare-haren ta'addanci da suka hana manoma zuwa gona ballantana shuka da girbi.Ku latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken shirin tare da Ahmed Abba.

página 2 de 2