Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Informações:

Sinopsis

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episodios

  • Kan halin rashin tsaron da arewa maso yammacin Najeriya ke ciki

    18/04/2024 Duración: 10min

    Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa da ake kira Global Rights ta bayyana cewa yankin arewa maso yammacin Najeriya shi ne mafi fuskantar ayyukan ta’addanci masu alaka da kashe-kashe ko garkuwa da mutane idan an kwatanta da yankin kudancin kasar. Rahoton da ya bayyana halin da ake ciki a yankin na arewa maso yammacin Najeriya da wani lamari mai tayar da hankali wanda kuma al’umma ba za su lamunci ci gaba da wanzuwarsa ba, ya ce wajibi ne mahukuntan kasar su lalubo hanyoyin warware matsalolin wannan yanki.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • An cika shekara guda da fara yakin kasar Sudan

    16/04/2024 Duración: 10min

    A farkon wannan makojn ne yakin da ake gwabzawa a Sudan tsakanin sojojin kasar karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun RSF da ke karkashin Mohamed Hamdan Dagalo ke cika shekara guda. Rikicin da aka faro a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2023, ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da kuma raba miliyoyi da muhallansu, wanda a yanzu MDD ta ce akwai barazanar barkewar yunwa a kasar.Bangarori da dama ne dai suka yi yunkurin warware wannan rikici amma abin yaci tura.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.

  • Kan cika shekaru 10 da sace daliban Chibok da Boko Haram ta yi

    15/04/2024 Duración: 09min

    Yayin da aka cika shekaru 10 da sace dalibai a makarantar sakandiren 'yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, har yanzu akwai matan kusan 100 da ke tsare a hannun mayakan Boko Haram da suka yi garkuwa da su. Gwamnatin kasar dai na ci gaba da ikirarin cewa, tana iya bakin kokarinta wajen ganin an sako sauran 'yan matan da ke hannun mayakan.Abin tambayar ita ce, wannen hali iyayen yara da ke hannun mayakan ke ciki?Yaya makomar ilimi take a Najeriya, tun daga lokacin da Boko Haram suka kafa tarihin sace dalibai kawo yanzu?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    12/04/2024 Duración: 09min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    05/04/2024 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • Gamnonin Najeriya sun ciyo bashin kusan dala biliyan biyu

    03/04/2024 Duración: 10min

    Kasa da shekara guda bayan rantsar da sabbin gwamnonin Najeriya, 13 daga cikin su, sun ciyo bashin da yawan sa ya kai dala biliyan 2 daga kasashen waje ko kuma cibiyoyin bada lamuni daban-daban. Cin bashi a tsakanin gwamnatocin Najeriya ba sabon abu bane sai dai kuma abinda ‘yan kasar ke fargaba shine idan har an ciyo wannan adadin bashi a kasa da shekara guda, nawa za’a ciwo cikin shekaru 4.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa.

  • Sabon shugaban Senegal ya karbi rantsuwar kama aiki

    02/04/2024 Duración: 10min

    A ranar Talata ne aka rantsar da sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, wanda ya lashe zaben kasar a makon da ya gabata da kaso sama da 54 cikin 100 na yawan kuri’u sama da miliyan 7 da aka kada. Faye shine shugaba mafi kankantar shekaru a Afrika, kuma ya lashe zaben ne a wani yanayi da kasar ke cikin chukumurdar siyasa.Matashin ya zama shugaban kasa ne kasa da makonni biyu bayan fitowar sa daga gidan yari.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Yadda Kiristoci suka gudabnar da bikin Easter a fadin duniya

    01/04/2024 Duración: 09min

    Kiristoci a fadin duniya su na gudanar da bukukuwan Easter, ranar mai mahimanci da ke zagayowa duk shekara don tunawa da sadaukarwar da Isa Almasihu ya yi domin duniya, wadda a cikin sakon Paparoma Francis yai kira ga duniya bisa kiyaye afkuwar yaki kowanne iri. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Sakamkon zaben kasar Senegal na ci gaba da daukar hankali

    27/03/2024 Duración: 09min

    Dan takarar adawa Bassirou Diomoye Faye wanda ke tsare a gidan yari har zuwa jajibirin zabe, zai kasance shugaban kasar Senegal kamar yadda alkaluman zaben da aka yi ranar lahadin da ta gabata ke nunawa. Shin wanne irin gagarumin sauyi aka samu a fagen siyasar kasar Senegal inda dan adawa ya kayar da dan takarar jam’iyyar da ta share shekaru 12 kan karagar mulki?Wanne irin mataki al'ummar Senegal suka dauka na samar da wannan sauyi cikin kankanin lokaci, musamman lura da irin rikice-rikicen da kasar ta yi fama da su a baya, amma duk da haka aka yi wannan zabe a cikin kwanciyar hankali?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Karin kudin aikin Hajjin bana a Najeriya ya shafi maniyyata da dama

    26/03/2024 Duración: 10min

    Hukumar alhazai a Najeriya, ta sanar da karin kusan Naira milyan biyu a kan kujerar aikin hajjin bana ga maniyatan da suka riga suka zuba kudadensu. Wannan dai mataki ne da ya yi matukar bai wa jama’a mamaki, tare da kara haifar da fargar cewa dubban maniyata ba za su iya sauke faralin na shekarar bana ba.Abin tambayar shine, wane tasiri wannan mataki zai yi a kan maniyatan Najeriya na shekarar bana?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Yadda rundunar tsaron Najeriya ta ceto daliban Kuriga

    25/03/2024 Duración: 10min

    Rundunar tsaron Najeriya ta sanar da ceto 137 daga cikin dalibai 287 da aka sace a makarantar garin Kuriga da ke jihar Kaduna  bayan share tsawon makonni biyu a hannun ‘yan bindiga. Sanarwar da rundunar sojin ta fitar na cewa an ceto mutanen ne a wani wuri da ke cikin jihar Zamfara.Abin tambayar shine, ko meye makomar sauran mutane 151 da aka sace lokaci guda tare da wadanda aka kubutar?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    22/03/2024 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin Masu Saurare: Tsananin zafi mafi muni a shekarar 2024

    20/03/2024 Duración: 10min

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce shekarar da ta gabata ita ce mafi zafi da duniya ta gani, sai dai ta yi gargadin cewa 2024 za ta fi bara muni. A wani rahoton shekara-shekara da Majalisar ta fitar, ta ce dukannin binciken da ta gudanar ya nuna cewa 2023 itace mafi zafi a tarihin duniya.Rahoton binciken ya kuma ce shekaru biyun da suka gabata, sune mafi tsananin zafi cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da ake fargabar zafin zai ci gaba da tsananta a bana.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Nasirudden Muhammad.

  • Yadda katsewar layukan sadarwa na karkashin teku ya shafi Afirka

    19/03/2024 Duración: 10min

    Yau kusan kwanaki 6 kenan da kasashe da dama na Afirka ke fama da matsalar Internet, a wani abu da masana ke cewa ya samo asali ne daga katsewar layukan sadarwa na karkashin teku. Duk da cewa ba a bayyana wa duniya lokacin da za a dauka kafin shawo kan wannan matsala ba, amma bisa ga dukan alamu tangardar za ta iya daukar dogon lokaci kafin a shawo kansa.Abin tambayar ita ce, ko yaya wannan matsala ta internet ke shafar harkokinku jama'a na yau da kullum?

  • Matsalar garkuwa da mutane na kara kamari a arewacin Najeriya

    11/03/2024 Duración: 10min

    A Najeriya an shiga wani yanayi na fargaba da kuma tsoro lura da yadda ‘yan bindiga suka tsananta dabi’ar yin garkuwa da mutane masu tarin yawa a lokaci daya musamman ma a yankin arewacin kasar. A cikin makon da ya gabata kawai, sama da mutane 5,00 ne aka yi garkuwa da su, da suka hada mata ‘yan gudun hijira a jihar Borno, da daliban firamire da sakandare a jihar Kaduna, sai kuma almajiran tsagaya a jiyar Sokoto.Abin tamabayar shine, shin me ke faruwa ne musamman ta la’akari da yadda hukumomin tsaro suka gaza bai wa jama’a kariya a sassan kasar?Anya kuwa gwamnati na da wani tsari da za ta iya aiwatarwa don tunkarar wannan matsala?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    08/03/2024 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • Najeriya: Tsadar rayuwa ta tilastawa mutane satar abinci a rumbunan gwamnati

    05/03/2024 Duración: 10min

    A Nageriya daidai lokacin da ake fama da fatara da kuma tsadar rayuwa,  jama’a sun bullu da wani sabon salo na yin wasoson abincin da aka jibge a cikin rumbunan da aka bayyana cewa mafi yawan su mallakar gwamnati ne  Abin tambayar shine, mecece makomar wannan bakuwar dabi’a da wasu ‘yan Najeriya suka bullo da ita a cikin wannan yanayi na fatara da kuma tsadar rayuwa?Wadanne matakai suka kamata a dauka domin shawo kan wannan matsala da ka iya rikidewa domin kasancewa barazana, hattama ga bangaren tsaron kasar.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    01/03/2024 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

  • Kan zanga-zangar da kungiyar kwadagon Najeriya ta gudanar

    28/02/2024 Duración: 09min

    Kungiyar kwadago a Najeriya ta sanar da janye zanga-zangar da ta shirya gudanarwa ranar Laraba kan matsalar tsadar rayuwa. Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar ta shirya gudanar da zanga-zangar na tsawon kwanaki biyu, inda ta fara aiwatar da kudirin nata a ranar Talata.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Kan janyewar takunkumin ECOWAS ga kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso

    26/02/2024 Duración: 08min

    Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ko CEDEAO a taron da ya gudana a ranar Asabar a Abuja sun yanke shawarar dage wani kaso mai yawa na takunkumin da aka kakabawa Nijar. Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, wadanda musamman suka juya wa Faransa baya, kuma suka matsa kusa da Rasha, sun hade a cikin kawancen kasashen Sahel (AES).Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.

página 1 de 2