Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Kwamared Nuhu Abayo Toro: Kan matatar mai ta Fatakwal
10/12/2024 Duración: 03minƘungiyar Kwadago ta Najeriya ta ziyarci matatar man fetur ta birnin Fatakwal bayan gwamnatin ƙasar ta ce matatar ta fara aiki gadan-gadan. Domin jin yadda wannan matata ta fara aiki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Kwamare Nuhu Abayo Toro, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar kwadagon da suka ziyarci matatar.Ku lata alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
-
Irbaɗ Ibrahim: Yadda John Mahama ya lashe zaɓen Ghana
09/12/2024 Duración: 03minAn kammala zaɓen shugaban ƙasar Ghana, ba tare da fuskantar wata matsala ba, duk da cewa an yi hasashen za'a iya fuskantar tashin tashina a lokacin zaɓen. Sakamkon zaɓen na ƙarshen mako ya nuna cewa tsohon shugaban kasa John Mahama ne ya lashe saben, kuma tuni ɗan takaran jam’iyya mai mulki, Mahamudu Bawumia ya taya shi murya, abin da ke nuni da cewa ya amince da shan kaye.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar Bashir Ibrahim Idris tare da Alh. Irbaɗ Ibrahim, masanin siyasa a Ghana
-
Ambasada Abubakar Chika kan martanin da ake maidawa na kifar da gwamnatin Assad
09/12/2024 Duración: 03minƘasashen duniya sun fara mayar da martani dangane da nasarar da ƴan tawaye suka samu na karɓe iko da birnin Damascus tare da tserewar shugaba Bashar Al Assad. Yayin da wasu ke murna dangane da kawo ƙarshen Assad a karagar mulki, wasu kuma na bayyana damuwa akan makomar yankin Gabas ta Tsakiya. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran, Ambasada Abubakar Chika. Ku latsa alamar sauti domin jin yadda zantawarsu ta gudana........
-
Mun biya ƴan bindiga kafin mu yi noma amma sun hana mu girbi - mazauna Zamfara
05/12/2024 Duración: 03minMazauna yankunnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na ci gaba bayyana irin halin kuncin rayuwa da suka samu kansu sakamakon yadda suke biyan ƙudi ga ƴan bindiga kafin su yi noma a daminar da suka gabata, yanzu kuma lokacin girbi ƴan bindigar sun hana su zuwa girbi da kwaso amfanin gonar sai sun biya.Wannan matsala ta yi sanadiyar talauta akasarin mutanen da ke wannan yankin. Dangane da wannan batu ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, kuma ga abinda ya shaida masa.
-
Satar manyan jami'an gwmanati na ci wa 'Yan Najeriya tuwo a ƙwarya
04/12/2024 Duración: 03min'Yan Najeriya na ci gaba da bayyana bacin ransu danagane da satar da wani tsohon babban jam'in gwamnati ƙasar ya yi, ya kuma gina gidaje sama da 750. Tuni kotu ta ƙwace gidajen da kuma mallakawa gwamnati. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Bala Ibrahim mai sharhi kan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantawar tasu ta gudana. Sai a latsa alamar sauti domin sauraron shirin.
-
Satar manyan jami'an gwamnati na ci wa 'yan Najeriya tuwo a ƙwarya
04/12/2024 Duración: 03minƳan Najeriya na ci gaba da bayyana ɓacin ransu dangane da satar da wani tsohon babban jami'in gwamnatin ƙasar ya yi, ya kuma gina gidaje sama da 750. Tuni kotu ta ƙwace gidajen da kuma mallakawa gwamnati, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Bala Ibrahim mai sharhi kan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantarwarsu ta gudana.
-
Tattaunawa da Muhammad Dahiru Dan Adam kan ƙalubalen naƙasassu a jihar Lagos
03/12/2024 Duración: 03minYau ce ranar da Majalisar ɗinkin duniya ta ware domin tunawa da halin da masu buƙata ta musamman ke ciki da kuma duba hanyoyin da za a inganta rayuwarsu. Karibullahi Abdulhamid Namadobi ya yi tattaki zuwa wani gida a jihar Lagos mai ɗauke da irin waɗannan mutanen sama da dubu 3 da suka fito daga yankunan arewacin Najeriya. Ga yadda zantawarsa ta gudana da guda cikin shugabanninsu Muhammad Dahiru Dan Adam.
-
Nasir Kabir kan yajin aiki a wasu jihohin Najeriya kan mafi ƙarancin albashi
02/12/2024 Duración: 03minYau ma'aikan gwamnati a jihohi kusan 15 na Najeriya ke fara yajin aiki saboda ƙin biyansu mafi ƙarancin albashin naira dubu 70 da sabuwar doka ta tanada. Ƙungiyar kwadago ta ƙasar ta bai wa jihohin umarnin fara yajin aikin. Saboda haka Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Sakataren tsare tsaren ta Comrade Nasir Kabir. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana........
-
Ngozi Okonjo Iweala ta sake zama shugabar WTO
29/11/2024 Duración: 03minHukumar Kasuwanci ta duniya WTO ta bai wa tsohuwar ministan kudin Najeriya Ngozi Okonjo Iweala wa'adi na 2 na shekaru 4, yayin da ta kawo karshen wa'adinta na farko. Wannan ya biyo bayan kasancewarta 'yar takara daya tilo da ta sake neman mukamin.Domin tasirin wannan nadi da kuma kalubalen dake gabanta, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Isa Abdullahi, masanin tattalin arziki a Najeriya.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Tattaunawa da Mele Kyari kan fara aiki a matatar mai ta Fatakwal da NNPCL ta sanar
27/11/2024 Duración: 03minA Najeriya bayan shafe shekaru da dama ana gyaran matatar man fetur na ƙasar da ke birnin Fatakwal a jihar Ribas, kamfanin man fetur na kasar NNPCL ya sanar da kammala gyarar a ranar Talata, inda ya kuma ce ba tare da wani bata lokaci ba tuni aka fara dakon man.NNPCL ya kuma shaida cewa sauran matatun mai na ƙasar, wato na Warri da Kaduna ma za su fara aiki ba tare da sanar da takamammen ranar da hakan zai kasance ba. Wakilinmu na Abuja, Mohammed Sani Abubakar ya tattaunawa da shugaban kamfanin na NNPCL Mele Kyari. Ku latsa alamar sauti domin jin hirar da aka yi da shi...
-
Dr. Kasum Kurfi kan rahotan NBS na farfadowar tattalin arzikin Najeriya
26/11/2024 Duración: 03minHukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 3.46 a rubu'i na uku na wannan shekarar ta 2024, wato tsakanin watan Yuli zuwa Satumba. A rahoton da ta fitar ranar Litinin, NBS ta ce yawan masara aikin yi ma ya ragu a Najeriya. Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dr Kasum Garba Kurfi.
-
Sanata Umar Ibrahim Tsauri kan matsayar gwamnonin PDP halin da Najeriya ke ciki
25/11/2024 Duración: 03minA ƙarshen makon da ya gabata ne gwamnonin PDP suka gudanar da taronsu a jihar Filato, wanda ya tattauna halin da Najeriya ke ciki da kuma makomar jam'iyyarsu. Bayan kammala taron gwamnonin sun buƙaci shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da ya sake nazari kan manufofinsa na tattalin arziki saboda illar da yake yiwa talakawa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP na ƙasa, Sanata Umar Ibrahim Tsauri. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawarsu..........
-
Farfesa Abdullahi Zuru kan martanin ƙasashe bayan hukucin ICC na kama Netanyahu
22/11/2024 Duración: 03minAna ci gaba da samun martani daban daban dangane da umarnin kotun duniya ta ICC na bada sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant da kuma shugaban Hamas Mohammed Deir saboda aikata laifuffukan yaki. Yayin da wasu ke murna da matakin, wasu kuma irinsu Amurka na watsi da shi. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar shari'a Farfesa AShehu Abdullahi zuru, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Amb Ibrahim Kazaure kan cikar wa'adin da ECOWAS ta baiwa Mali, Nijar da Burkina
21/11/2024 Duración: 03minYanzu haka saura watanni 2 kafin cikar wa'adin shekara guda da ECOWAS ta gindaya domin duk wani mai shirin fita daga cikin ta, sakamakon shelar da Jamhuriyar Nijar da ƙawayenta Mali da Burkina Faso suka yi na janyewa daga cikin ta. Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ke nuna janye matakin, ya yin da aka tabbatar da cewar har yanzu wakilan Nijar na aiki a hukumomin na ECOWAS. Domin duba wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon ministan ayyuka na musamman a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu........
-
Alhaji Adamu Muhammad Madawa kan rashin maida mulki hannun farar hula a Nijar
20/11/2024 Duración: 03minKusan shekara guda da rabi da juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, har ya zuwa yanzu babu wani shiri daga sojojin na mayar da mulki ga fararen hula. Wannan ya sa wasu daga cikin jama'ar ƙasar gabatar da buƙata ga sojoji da su sake tunani akai domin bai wa jama'a damar zaɓin shugabannin da suke so. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Alhaji Adamu Muhammad Madawa, daya daga cikin shugabannin ƴan Nijar mazauna Najeriya. Ku latsa alamar sauti dominjin yadda zantawarsu ta gudana........
-
Malam Hussaini Manguno kan ziyarar da tawagar Najeriya ta kai Chadi
19/11/2024 Duración: 03minTawagar gwamnatin Najeriya ta ziyarci ƙasar Chadi, inda ta gana da shugaban kasa Mahamat Idris Deby sakamakon barazanar da ya yi na janye dakarunsa daga rundunar hadin gwuiwar dake yaki da boko haram. Tawagar a ƙarƙashin Malam Nuhu Ribadu, ta kunshi hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa. Bayan ganawar Bashir Ibrahim Idris ya tatatuna da masanin harkar tsaro Malam Hussaini Manguno. Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana........
-
Dr Isa Abdullahi kan inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da India
18/11/2024 Duración: 03minA karshen makon da ya gabata ne Firaministan India Narendra Modi ya ziyarci Najeriya domin inganta dangantakar ƙasashen biyu musamman a ɓangaren kasuwanci. Alkaluma sun bayyana cewar kamfanonin India sama da 200 sun zuba jarin da ya zarce dala biliyan 27, yayin da Modi ke goyan bayan Najeriya wajen ganin ta zama mamba a kungiyar G20 da BRICS. Dangane da ziyarar Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Isa Abdullahi. Ku latsa alamar sauti domin jin yadda zantawarsu ta gudana............
-
Ambasada Abubakar Chika kan buƙatar ƙorar Isra'ila daga Majalisar Ɗinkin Duniya
14/11/2024 Duración: 03minShugabannin ƙasashen Musulmi da na Larabawa, sun kammala taronsu da gabatar da buƙatar korar Isra'ila daga Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan gillar da ta yi a Gaza. Taron ya kuma amince da wasu ƙudurori daban daban da su kai ga tabbatar da ƙasar Falasɗinu. Dangame da matakan da shugabannin suka ɗauka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Abubakar Chika, tsohon jakadan Najeriya a Iran. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawar ta su..........
-
Alhaji Muhammadu Magaji kan saye kayan amfanin gona a Najeriya
13/11/2024 Duración: 03minMazauna yankin arewacin Najeriya na bayyana damuwa kan yadda kamfanoni da ƴan kasuwa ke rige rigen sayen kayan abinci a hannun manoma. Masana na bayyana fargabar cewar matakin zai sanya kayan abincin ya yi tsada a daidai lokacin da jama'a ke fama da tsadar rayuwa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Muhammadu Magaji, Sakataren tsare tsare na ƙungiyar manoman Najeriya dangane saye kayan abincin. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawar ta su........
-
Tattaunawa da Abdullahi Idris Zuru kan harin Lakurawa a jihar Kebbi
11/11/2024 Duración: 03minSabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa da ta bayyana a makwannin baya-bayan nan cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya ta hallaka aƙalla mutane 15 a harin da ta kai garin Mera na jihar Kebbi baya ga kora tarin dabbobin jama’a.Bayanai sun ce an yi artabu tasakanin yan ta’addan da mutanen gari gabanin tserewarsu. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kakakin gwamnatin jihar kebbi Abdullahi Idris Zuru wanda ya bayyana cewa tuni gwamnati ta ɗauki matakan baiwa jama'a kariya baya ga aikewa da twaga don bin sahun ƴan ta'addan.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.