Sinopsis
Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.
Episodios
-
Taba ka Lashe 15.09.2022
27/09/2022 Duración: 09minSaurari shirin don jin yadda miliyoyin al'umma 'yan kabilar Tubawa da suka warwatsu a kasashe da dama na Kudu da hamadar Sahara suka gudanar da bikin ranar Tubawa.
-
Taba Ka Lashe: 14. 09. 2022
20/09/2022 Duración: 09minKo kun san abin kidan da ake kira da Kuntigi da ma su kanus makadan Kuntigin? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan kidan da makadan.
-
Taba Ka Lashe: 07.09.2022
13/09/2022 Duración: 09minKo kun san cewa ana gudanar da babban taro da ke hada kan dukkannin majami'un addnin Kirista na fadin duniya duk shekara? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan taro, musamman yadda mabiya addnin Kirista daga Najeriya da suka halarci taron suka nemi a tallafawa kasar da ke cikin halin rashin tabbas.
-
Taba Ka Lashe: 31.08.2022
06/09/2022 Duración: 09minKo kun san akwai wasa tsakanin kaka da jika a kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan al'ada.
-
Taba Ka Lashe: (24.08.2022)
30/08/2022 Duración: 09minKo kun san wasu malaman jami'a a Katsina sun koma sana'ar gado sakamakon yajin aikin kungiyra malaman jami'o'i ta kasar ASUU? Ku biyo mu domin jin wanda ya rungumi sana'arsa ta gado wato wanzanci.
-
Taba Ka lashe: Makwabtaka
23/08/2022 Duración: 09minZamani ya taho da abubuwa da dama, kuma wannan shirin ya fito da bambancin yanayin zamantakewar al'ummar Hausawa a can baya da kuma na wannan zamanin.
-
Shirin Taba Ka Lashe kan kudin shara
09/08/2022 Duración: 09minShara wata al'ada ce da malam Bahaushe ya kirkira tare da dangantawa da lokacin kololuwa na ibada bayan da ya karbi addinin Muslunci.
-
Taba Ka Lashe: 06.07.2022
12/07/2022 Duración: 09minShirin ya yi nazari kan kidan kalangu, ku biyo mu domin ku rausaya.
-
Taba Ka Lashe: Sauye–sauyen zamani ga al’adar aure a kasar Hausa
21/06/2022 Duración: 09minShirin Taba Ka Lashe kan sauye–sauyen zamani ga al’adar aure a kasar Hausa
-
Taba Ka Lashe: 08.06.2022
14/06/2022 Duración: 09minShirin ya yi nazari kan yadda mutane musamman a kasar Hausa, ke yin adashi domin taimakon kansu.
-
Taba Ka Lashe (25+26.05.2022)
31/05/2022 Duración: 09minKungiyar DRPC na daga cikin kungiyoyi a jihar Jigawa da ke fadi-tashi wajen ganin sun ciyar da fannin ilimi gaba a Najeriya.
-
Taba Ka Lashe (18.05.2022)
24/05/2022 Duración: 09minShirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya garzaya jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, inda ya yi nazari kan al'adar maita.
-
Taba Ka Lashe: Sallah a masarautar Abzin
10/05/2022 Duración: 09minSaurari yadda aka gudanar da bikin Sallah karama a fadar sarkin Abzin na jihar Agadez. An shafe kwanaki uku ana bukukuwan al’adar da ke kayatar da jama’a.
-
Taba Ka Lashe: Batun amfani da harshen gida a Jamhuriyar Nijar
12/04/2022 Duración: 09minShirin ya yada zango a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar inda muka duba batun yadda iyaye ke sakaci wajen koyar da yara harshen gida.
-
Taba Ka Lashe 16.03.2022
22/03/2022 Duración: 09minAl'adar bikin aure a kasar Guddirawa da ke jihar Bauchin Najeriya mai dumbin tarihi.
-
Taba Ka Lashe: Al'adar bikin aure a Guddiri
15/03/2022 Duración: 09minAure na daya daga cikin al'adun da Guddurawa suke masa hidima ta gani a fada fiye da duk wata al'adar su, kama daga farkon nema tsakanin saurayi da budurwa har zuwa lokacin bayarwa da mai gaba daya lokacin bikin auren. Kuma har zuwa yanzu guddurawa ba su bari ba. Wannan shi ne batun a shrin Taba Ka ashe na wannan mako ya yi duba a kai. Daga kasa za a iya sauraon sauti
-
Taba Ka Lashe: Al'adar bikin aure a Guddiri
15/03/2022 Duración: 09minAl'adar bikin aure a Guddiri a Jihar Bauchi dadaddiyar masarauta ce mai dumbin tarihi, kuma guddurawa suna da wasu fitattun al'adunsu da suka banbanta su da sauran masarautun Bauchi.
-
Taba Ka Lashe: 02.03.2022
08/03/2022 Duración: 09minKo har yanzu ana amfani da wakokin gargajiya da kayan kidan harshen Hausa a kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: Rayuwar Musulmi da Kirista
15/02/2022 Duración: 09minMusulmi da Kirista a Jihar Filaton Najeriya na zaune a unguwani dabam-dabam sabanin yadda a baya al'ummomin biyu ke zaune wuri guda suna cudanya.
-
Taba Ka Lashe 02.01.2022
08/02/2022 Duración: 09minShirin na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan kirari. Ya al'adar kirari take a kasashen Afirka?