Sinopsis
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episodios
-
Fatanmu wasan Damben gargariya ya shiga wasannin Olympics - Dambe Warriors
10/06/2024 Duración: 10minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan ci gaban da wasan Damben Gargajiya ke samu a kasar Hausa. Akwai kungiyoyi da dama da a yanzu suka shiga cikin sabgar wasan dambe wanda kuma hakan ke kara mata tagomashi dama jawo ra’ayin wadanda da basa ciki shiga cikinta gadan-gaban. Dambe Warriors na daga cikin kungiyoyi da ke suka jima suna shirya wasan inda 'yan wasan ke samun albashi mai tsoka a mataki daban-daban. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Mahawara kan yadda kungiyar Madrid ta lashe kofin zakarun Turai
03/06/2024 Duración: 09minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon, ya maida hankali ne kan wasan karshe na gasar zakarun Turai wanda kungiyar Real Madrid ta lashe karo na 15 a tarihi, bayan doke Brussia Dortmund, abunda ya maida ita kungiyar data fi kowwacce nasarar dauke wannan kofi mafi girman dearaja a Turai. Gabanin wasan dai ana ganin da wahala Madrid din ta iya samun nasara lura da yadda Dortmund ta zo matakin wasannan na karshe, duk kuwa da cewar tarihin Madrid din na nuna tafi iya lashe kofin data sha wahalar zuwa wasan karshe.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....
-
Bitar yadda aka kammala kakar wasanni ta bana
27/05/2024 Duración: 10minShirin a wannan mako shirin ya yi sharhi ne kan yadda aka kammala gasar La liga da wasan karshe na kofin FA da sauran abubuwan da suka faru a karshen wannan mako. Haka nan shirin ya yi tsokaci game da babban wasan da za a iya cewa ya rage a nahiyar Turai a wannan kaka wato wasan karshe na gasar Zakarun nahiyar da za ayi tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikken shirin tare da Khamis Saleh.....
-
Manchester City ta kafa tarihi bayan lashe kofin Firimiyar Ingila karo 4 a jere
20/05/2024 Duración: 10minShirin duniyar wasanni na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda aka kammala gasar Firimiyar Ingila, musamman yadda kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kafa sabon tarihin lashe gasar karo 4 a jere.