Sinopsis

Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.

Episodios

 • Tambaya da Amsa - Maanar G5 da yankin Sahel

  Tambaya da Amsa - Ma'anar G5 da yankin Sahel

  25/01/2020 Duración: 20min

  Masu sauraren Rfi Hausa ,sun nemi a basu karin haske dangane da Yankin G5 Sahel wane yanki ake kira Sahel shin kasashe nawa ne a cikin wannan yankin kuma a ina ya samo wannan suna? Mickael Kuduson a cikin shirin tambaya da amsa ya jiyo ta bakin masana dangane da wadana tambayoyi daga masu saurare a cikin shirin tambaya da Amsa daga nan sashen hausa na Rfi.

 • Tambaya da Amsa - Tarihin Shahararren Mawakin nan Abubakar Mai Bibbiyu

  Tambaya da Amsa - Tarihin Shahararren Mawakin nan Abubakar Mai Bibbiyu

  18/01/2020 Duración: 19min

  Gambo Damagaram da Wari Malam Bare Barezuwa da Bamaini Hannami Mormotuwa duka Jamhuriya Nijar. Tarihin Shararran Mawakin nan Abubakar Mai Bibbiyu suke nema,Mickael Kuduson ya duba tambaya ,ga kuma hirar da ya samu da Abubakar Mai Bibbiyu cikin shirin tambaya da amsa.

 • Tambaya da Amsa - Alfanun shan nonon rakumi

  Tambaya da Amsa - Alfanun shan nonon rakumi

  28/12/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin tambaya da amsa ,wasu daga cikin masu saurare sun bukaci samun karin haske dangane da alfanun shan nonon rakumi. Mickael Kuduson ya jiyo ta baki masana ,da suka duba wasu daga cikin tambayoyin ku masu sauraren RFI a cikin wannan shirin.

 • Tambaya da Amsa - Amsar tambaya kan alakar sanyin hunturu da karuwar masu tabin hankali

  Tambaya da Amsa - Amsar tambaya kan alakar sanyin hunturu da karuwar masu tabin hankali

  21/12/2019 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da amsa a wannan makon tare da Michael Kuduson ya amsa muhimman tambayoyi ciki har da tambayar da ke neman karin bayani kan alakar yawaitar samun masu tabin hankali a lokacin hunturu.

 • Tambaya da Amsa - Aman wuta daga dutse cikin ruwa?

  Tambaya da Amsa - Aman wuta daga dutse cikin ruwa?

  14/12/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin tambaya da Amsa, za ku ji ko a ina aka kwana dangane da wasu daga cikin matsalolli da suka jibanci kiwon lafiya,musaman shan suga daga dan Adam, wasu daga cikin masu saurare sun nemi ji ko mai ya sa ake samun aman wuta daga dutse cikin ruwa. Mickael Kuduson ya ji ta bakin masana a cikin shirin tambaya da Amsa.

 • Tambaya da Amsa - Amsar tambaya kan matsayin yankin Hong Kong mai kwarya-kwaryar yancin karkashin China

  Tambaya da Amsa - Amsar tambaya kan matsayin yankin Hong Kong mai kwarya-kwaryar 'yancin karkashin China

  07/12/2019 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya amsa muhimman tambayoyi ga masu sauraro ciki har da matsayin yankin Hong Kong ga gwamnatin China.

 • Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan alfanun wanka da ruwan zafi ga jikin dan adam

  Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan alfanun wanka da ruwan zafi ga jikin dan adam

  30/11/2019 Duración: 20min

  Shirin Tambaya da Amsa a wannan lokaci ya amsa muhimman tambayoyin da kuka aiko mana ciki har da tambayar da ke neman sanin muhimmancin amfani da ruwan zafi ga lafiyar bil'adama. Ayi saurare Lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Adam A Zango ya amsa wasu daga cikin tambayoyin RFI

  Tambaya da Amsa - Adam A Zango ya amsa wasu daga cikin tambayoyin RFI

  23/11/2019 Duración: 20min

  A cikin shirin tambayoyin ku masu saurare,Mickael Kuduson ya nemi jin ta bakin masana da ya dace su kawo muku karin haske dangane da wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko. Haka zalika zaku ji hirar darediyon Faransa na rfi yayi da Adam A Zango.

 • Tambaya da Amsa - Karin bayani kan kan rabe-raben aikin hako mai a sassan Najeriya

  Tambaya da Amsa - Karin bayani kan kan rabe-raben aikin hako mai a sassan Najeriya

  16/11/2019 Duración: 20min

  Shirin Tambaya da Amsa a wannan makon ya tattauna da masana kan batutuwan da masu sauraro suka nemi karin haske akai, ciki har da karin bayani kan rabe-raben aikin hako mai a sassan Najeriya, da kuma tasiri rufe kan iyakokin kasa da kuma kasashen da suka yi amfani da salon wajen karfafa tattalin arzikinsu.

 • Tambaya da Amsa - Rikicin siyasa

  Tambaya da Amsa - Rikicin siyasa

  09/11/2019 Duración: 19min

  An taba samu wanda ya kalubalanci sakamakon zabe a tarihin Najeriya har ya kai ga zuwa kotu kamar yadda Atiku Abubakar ke yi? Idan har an taba, ya aka kare? Shin a wane irin kotu ake kai wannan korafi? Mickael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyi masu saurare,tareda duba amsoshin su da masana.

 • Tambaya da Amsa - Karin bayani kan manhajar Google Play Store

  Tambaya da Amsa - Karin bayani kan manhajar 'Google Play Store'

  26/10/2019 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon yayi karin bayani kan batutuwa da dama dangane da  manhajar 'Google Play Store', sai kuma wasu karin tambayoyin da masu sauraro suka aiko.

 • Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan manhajar kudi ta Intanet wato Crypto currency

  Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan manhajar kudi ta Intanet wato Crypto currency

  19/10/2019 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da amsa tare da Micheal Kuduson ya amsa manyan tambayoyo ciki har da karin bayani kan manhajar kudin intanet na Crypto currency. Ayi saurare Lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Kabila guda ce Tuareq da Buzaye Da kuma Abzinawa?

  Tambaya da Amsa - Kabila guda ce Tuareq da Buzaye Da kuma Abzinawa?

  12/10/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin Amsa da tambaya daga nan sashen hausa na rediyon Faransa Mickael Kuduson ya mayar da hankali zuwa wasu daga cikin tambayoyin ku masu saurare kamar haka: Kabila guda ce Tuareq da Buzaye da kuma Abzinawa? Wace dangantaka wadannan kabilu keda shi da larabawa? Shin bayan wadannan akwai wasu kabilun farar fata wadanda ba larabawa ba a kasashen Afrika.

 • Tambaya da Amsa - Dalilan dake haddasa jinkiri da rashin haihuwa

  Tambaya da Amsa - Dalilan dake haddasa jinkiri da rashin haihuwa

  05/10/2019 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa kamar yadda aka saba, ya amsa wasu tambayoyi da masu sauraro suka aiko, ciki har da neman karin bayani kan dalilan da suke haddasa matsalar jinkirin samun haihuwa da rashin ma baki daya.

 • Tambaya da Amsa - Dalilan rikicin kyamar baki a Afrika ta Kudu

  Tambaya da Amsa - Dalilan rikicin kyamar baki a Afrika ta Kudu

  21/09/2019 Duración: 20min

  Shirin Tambaya da Amsa kamar yadda aka saba, ya amsa wasu tambayoyi da masu sauraro suka aiko, ciki har da neman karin bayani kan dalilan matsalar kyamar baki a kasar Afrika ta Kudu.

 • Tambaya da Amsa - Cikakkiyar maanar juyin-juye hali

  Tambaya da Amsa - Cikakkiyar ma'anar juyin-juye hali

  31/08/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin tambayoyin da za ku ji amshoshin wasu daga cikin tambayoyin ku,wasu masu saurare sun bukaci sanin cikakkiyar ma'anar juyin-juye hali,ribarsa da illarsa da saurensu. Mickael Kuduson ya bincika tareda samu amsar wadanan tambayoyi.

 • Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan kasashen da ke da kujeran naki a Majalisar Dinkin Duniya

  Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan kasashen da ke da kujeran naki a Majalisar Dinkin Duniya

  24/08/2019 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa tare da Micheal Kuduson ya amsa muhimman tambayoyi a wannan mako, ciki har da amsar tambayar kasashen da ke da kujerar naki a Majalisar Dinkin Duniya, Ayi saurare Lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Karin haske kan mutuwar Osama bin Laden da kuma alakarsa da Amurka

  Tambaya da Amsa - Karin haske kan mutuwar Osama bin Laden da kuma alakarsa da Amurka

  17/08/2019 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa kamar, ya amsa wasu tambayoyi da masu sauraro suka aiko, ciki har da mutuwar Osama bin Laden da kuma alakarsa da Amurka, sai kuma bayani kan juyin juya hali, manufarsa, illoli da kuma amfaninsa.

 • Tambaya da Amsa - Amsar Tambayar dalilan da suka haddasa rikicin kasar Rwanda

  Tambaya da Amsa - Amsar Tambayar dalilan da suka haddasa rikicin kasar Rwanda

  03/08/2019 Duración: 20min

  Shirin Tambaya da amsa na wannan mako tare da Micheal Kuduson, ya bayar da amsa kan tambayar da ke neman sanin dalilan da suka haddasa rikicin kasar Rwanda shekaru kusan 25 da suka gabata, wannan dama sauran muhimman tambayoyi da amsa na tattare a cikin shirin, a yi saurare lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Likita ya amsa wasu daga ciki tambayoyi da suka shafi mata

  Tambaya da Amsa - Likita ya amsa wasu daga ciki tambayoyi da suka shafi mata

  27/07/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin Tambaya da amsa,likita ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da suka jibanci lafiyar  mace mai dauke da juna biyu,banda haka zaku ji koa ina aka kwana dangane da tarihin yan tagwaye dake magane kamar Shugaba Buhari a Najeriya.

página 1 de 5