Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin masu sauraro kan ranar masu buƙata ta musamman ta duniya

Informações:

Sinopsis

Kamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 3 ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar masu buƙata ta musamman, wato mutane da ke rayuwa da wata naƙasa a fadin duniya.Wannan shi ne maudu’in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau.Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Hauwa Halliru Gwangwazo: