Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Yadda katsewar layukan sadarwa na karkashin teku ya shafi Afirka

Informações:

Sinopsis

Yau kusan kwanaki 6 kenan da kasashe da dama na Afirka ke fama da matsalar Internet, a wani abu da masana ke cewa ya samo asali ne daga katsewar layukan sadarwa na karkashin teku. Duk da cewa ba a bayyana wa duniya lokacin da za a dauka kafin shawo kan wannan matsala ba, amma bisa ga dukan alamu tangardar za ta iya daukar dogon lokaci kafin a shawo kansa.Abin tambayar ita ce, ko yaya wannan matsala ta internet ke shafar harkokinku jama'a na yau da kullum?