Tambaya Da Amsa

Tambaya da Amsa: Amsar tambaya kan alakar girgizar kasa da aman wutar dutse

Informações:

Sinopsis

Shirin Tambaya da Amsa tare da Michael Kuduson a wannan mako ya amsa tambayoyin da masu saurare suka aiko, kuma a wannan makon za ku ji ci gaban amsa kan dalilan da ke haddasa girgizar kasa dama dangantaka tsakanin wannan matsala da aman wutar dutse da kasashe da dama ke fama da su. Haka zalika akwai amsa game da tarihin Marigayi Malam Amadou mai wa'azi na jihar Damagaram a Jamhuriyyar Nijar wanda ya koma ga mahaliccinsa a ranar 3 ga watan Satumbar da muke ciki ya na da shekaru 73 a Duniya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...........