Bakonmu A Yau

Irbaɗ Ibrahim: Yadda John Mahama ya lashe zaɓen Ghana

Informações:

Sinopsis

An kammala zaɓen shugaban ƙasar Ghana, ba tare da fuskantar wata matsala ba, duk da cewa an yi hasashen za'a iya fuskantar tashin tashina a lokacin zaɓen. Sakamkon zaɓen na ƙarshen mako ya nuna cewa tsohon shugaban kasa John Mahama  ne ya lashe saben, kuma tuni ɗan takaran jam’iyya mai mulki, Mahamudu Bawumia ya taya shi murya, abin da ke nuni da cewa ya amince da shan  kaye.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar Bashir Ibrahim Idris tare da Alh. Irbaɗ Ibrahim, masanin siyasa a Ghana