Lafiya Jari Ce

Yadda ake samun karuwar masu kamu wa da cutar cizon mahaukacin kare a Najeriya

Informações:

Sinopsis

Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan cutar cizon mahaukacin kare ko kuma Rabies a turance, bayan da bincike ya nuna cewar cutar na karuwa a Najeriya duk da cewa babu cikakkun alkaluman wadanda cutar ta shafa saboda karancin kawo rahoton cutar ga mahukunta. Sai dai wasu alkaluman hukumar dakile yaduwar cutuka ta Najeriyar NDDC sun nuna cewa daga shekarar 2017 zuwa 2022 akwai akalla mutane 998 da kuma karnuka 273 da suka harbu da cutar ta Rabies ko kuma cizon mahaukacin kare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....