Lafiya Jari Ce

Yadda hanyoyin gargajiya ke samun karbuwa wajen magance cutar sikila

Informações:

Sinopsis

Shirin 'Lafiya Jari Ce'  na wannan mako ya yi nazari ne kan hanyoyin gargajiya da ake bi wajen magance cutar  sikila  da kuma yadda al'umma suka karbi wadannan hanyoyi don samar wa kansu mafita. Shirin ya tattauna da masu maganin gargajiya da ke ikirarin cewa magungunansu na samar da waraka, kana ya gana da  liitocin zamani don neman karin haske a kan inda aka kwana wajen neman mafita a game da wannan cuta ta sikila.