Shirye-shiryen Matasa | Deutsche Welle

Informações:

Sinopsis

Shirye-shiryen DW Hausa a kan rayuwar matasa.

Episodios

  • Dandalin Matasa: Matasa da kangin talauci

    26/10/2023 Duración: 09min

    'Yan Najeriya akalla miliyan 71 na fama da matsanancin talauci a cewar bayanan World Poverty Clock ma'aunin talauci a duniya. Wai ma waye talaka? Mene ne kuma talauci?

  • Dandalin Matasa: 19.10.2023

    19/10/2023 Duración: 09min

    Shirin ya yi nazari kan batun yaki da talauci a tsakanin matasa, ta hanyar amfani da kafar Internet.

  • Dandalin Matasa: 12.10.2023

    12/10/2023 Duración: 09min

    Shirin ya ya da zango a Jamhuriyar Nijar don duba halin da matasa suka samu kansu a ciki a fannoni daban daban bayan da sojoji suka kawo karshen mulkin Mohamed bazoum na farar hula

  • Dandalin Matasa: 28.09.2023

    28/09/2023 Duración: 09min

    Ko matasan Najeriya ka iya kawo sauyi a fagen siyassar kasar, bayan da aka ji su tsit tun da aka kafa sabuwar gwamnati? Ko kuma dai suna awani yunkuri? Shirin Dandalin Matasa na wannan lokaci ya yi nazari a kai.

  • Darasin Rayuwa 20.09.2023

    22/09/2023 Duración: 09min

    Yadda mata bakar fata ke rayuwa ne a kasashen Larabawa musamman ma kasar Saudiyya.

  • Dandalin Matasa: 21.09.2023

    21/09/2023 Duración: 09min

    Ko yaya rayuwar 'yan gudun hijira ke gudana musamman ta fannin ilimi? Shirin Dandalin Matasa na wannan lokaci ya yi nazari kan batun ilimi ga 'yan gudun hijirar a Kamaru.

  • Dandalin Matasa: (14.09.2023)

    14/09/2023 Duración: 10min

    Shirin ya yi nazari kan yadda wani matashi ke taimakon 'yan uwansa matasa samun damarmaki da suka hadar da ayyuka ta kafar Internet.

  • Darasin Rayuwa: (06.09.2023)

    08/09/2023 Duración: 09min

    Shin kun taba tsintar kanku cikin bukata da 'yan uwa suka gaza taimaka muku, ko kuwa ku ne kuka gaza bayar da tallafi? Shirin Darasin Rayuwa ya yi nazari kan wannan batu.

  • Dandalin Matasa 07.09.2023

    07/09/2023 Duración: 09min

    Shirin na wannan lokaci, ya yi nazari ne kan gajiyar da matasan Najeriya suka ci ko akasin haka a kwanaki 100 na sabuwar gwamnatin kasar karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.

  • Intanet ya zama makamin killace wakokin matasa

    17/08/2023 Duración: 09min

    Mawaka masu tasowa na auna mizanin fikirarsu da kuma isar da sako harma da samun bayanai daga dandazon masoya ta tkafar You Tube. Ko 'yan nanaye na cin moriyar damarmalin dake tattare da wannan fasaha?

  • Dandalin Matasa: Auratayyan da ake yi a wannan zamanin wanda dai aka fi sani da an yi Wuff

    10/08/2023 Duración: 10min

    Auratayyan da ake yi a wannan zamanin wanda dai aka fi sani da an yi Wuff

  • Dandalin Matasa: 06.07.2023

    06/07/2023 Duración: 09min

    Ko kun san sabon taken kasa da aka yi a Jamhuriyar Nijar da ma yadda matasan kasar ke kallonsa? Shirin Dandalin Matasa yaa mayar da hankali a kai.

  • Darasin Rayuwa: 28.06.2023

    30/06/2023 Duración: 09min

    Wanne darasi wadanda suka saba yin layya suka koya a bana, sakamakon tsadar raguna da kkarancin kudi? Shirin Darasin Rayuwa.

  • Yunkuri na gyara dabi’un matasa

    22/06/2023 Duración: 09min

    Shirin Dandalin Matasa ya duba matakin jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya na fara wani yunkuri na gayara dabi’un matasa.

  • Dandalin Matasa: 15.06.2023

    15/06/2023 Duración: 09min

    Shirin ya yi nazari kan muhimmancin ranar 12 ga watan Yuni, ga matasan Najeriya da ma kasar baki daya.

  • Darasin Rayuwa 07.06.2023

    09/06/2023 Duración: 09min

    Shin Wani rin darasi za a iya koya daga irin zamantakewa da cudanya da ake yi da miliyoyin mutane da ake haduwa da su a yayin gudanar da aikin Hajji?

  • Dandalin Matasa

    25/05/2023 Duración: 09min

    A Najeriya, matasan da suka shiga harkokin zabe sun karu idan aka kwatanta da shekarun baya. Amma wasu me ya hana su taka rawar gani a fada a bana?

  • Darasin Rayuwa: 17.05.2023

    19/05/2023 Duración: 10min

    Shirin ya yi nazari kan matakin gyara ga dabi'un dalibai da jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchin Najeriya ta dauka.

  • Dandalin Matasa 11.05.2023

    11/05/2023 Duración: 09min

    a birnin Damagaram na Jamhuriyar Nijar, matasan da suka goge wajen taka leda na kwadayin rungumar buga kwallon kafa a matsayin sana'a a kasashen waje.

  • Darasin Rayuwa 13.04.2023

    14/04/2023 Duración: 09min

    Jinkiri a zirga-zirgar sufurin jiragen sama a Najeriya ya gawurtar da har ta kai fasinjoji na kwashe tsowon lokaci suna jiran jirgin ba tare da kwakwarar hujja ba.

página 2 de 3